Isa ga babban shafi

Taron BRICS ya sha alwashin tabbatar da tsarin kasuwancin bai-daya

Kasashen kungiyar BRICS, masu samun bunkasar arziki mafi girma a duniya na wannan zamani, su sha alwashin kare tattalin arzikinsu daga barazanar manufofin son kai a fagen huldar kasuwancin bai daya tsakanin kasashen duniya.

Shugabannin kasashen kungiyar BRICS tare da mukarrabansu a birnin Johannesburg na kasar Afrika ta Kudu. 27 ga watan Yuli, 2018.
Shugabannin kasashen kungiyar BRICS tare da mukarrabansu a birnin Johannesburg na kasar Afrika ta Kudu. 27 ga watan Yuli, 2018. REUTERS/Mike Hutchings
Talla

Kasashen da suka hada da Brazil, Rasha, India, China da kuma mai masaukin baki, Afrika ta Kudu sun shafe kwanaki uku ne suna gudanar da taron a Johannesburg, kafin cimma wannan matsaya, ta kare tattalin arzikinsu da kuma yakar barazanar ruguza tsarin cinikayyar bai daya, ba tare da sabawa dokokin hukumar kasuwanci ta duniya WTO ba.

Taron kasashen na kungiyar BRICS, da aka kawo karshensa a ranar Juma’a 27 ga watan Yuli na 2018, shi ne karo na farko da ya gudana, tun bayan da gwamnatin Amurka, karkashin Trump ta fara kokarin yiwa tsarin huldar kasuwanci bai daya tsakanin kasasshen duniya kwaskwarima, wanda shugaban na Amurka ya bayyana shi a matsayin wanda ke cutar da kasarsa.

Sai dai yayin taron na BRICS shugaban China Xi Jinping ya yi kira musamma ga majalisar dinkin duniya, da kuma Hukumar Kula da Kasuwanci ta Duniya WTO, da su kawo karshen duk wani shiri na tsarin baiwa tattalin arziki kasa kariya, irin na gwamnatin Amurka.

A nashi bangaren shugaban Rasha Vladmir Putin ya ya jaddada muhimmancin karfafa huldar cinikayyar da ke tsakanin kasashen kungiyar ta BRICS ne, inda yace karfin tattalin arzikin kasashen kungiyar Biyar shi ke rike da kashi 42, daga ciki 100 na tattali arzikin Duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.