rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Renon Faransa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Shugaba Sarkozy yayi tir da kisan wani Ba-Faranshe

media
Shugaban Nicolas Sarkozy Reuters / Philippe Wojazer

Shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy yayi alwashi ladabtar da kungiyar al-Qaeda kan kisan ba-Faranshe Michel Germaneau cikin yankin Sahel na Afrika.

A cikin jawabi ta tashar TV, shugaba Sarkozy yayi tir da kisan na jahiliya da akayi wa Germaneau dan shekaru 78 da haihuwa.

Shugaban ya bukaci Faransawa su kaucewa tafiya yankin na Sahel, inda kungiyar ta al-Qaeda ke kara samun gindin zama.

Tunda fari cikin wata nadaddiyar fira da tashar TV ta Al-Jazira ta yada a jiya Lahadi, shugaban kungiyar alka'ida reshen Magrib Aqmi, ya bayyana kashe Bafaranshen nan da kungiyar ta yi garkuwa da shi Michel Germaneau

shugaban kungiyar ta Aqmi Abou Moussab Abdel Wadud ya bayyana a cikin nadaddiyar muryar cewa sun zartar da hukumcin kisa a kan Michel Germaneau a ranar assabar 24 ga wannan watan Yuli domin yin ramuwar gayya ga yan uwansu guda 6 da suka rasa rayukansu a cikin farmakin da kasar Faransa ta kai, tare da sojojin kasar Mauritaniya a kan dakarun kungiyar alka'ida.