Isa ga babban shafi
Albaniya

Ana ci gaba da zanga-zanga a Albaniya

A yau Juma’a Dubun dubatar al’ummar kasar Albaniya ne suka yi gangami a Tirana babban birnin kasar a wata sabuwar zanga-zanga mako daya bayan gudanar da wata mummunar zanga-zangar adawa da gwamnatin kasar wacce ta yi sanadiyar rasa rayuka.Al’ummar kasar dai sun bijerwa kiran da kasashen yammaci suka yi na dakatar da zanga-zangar tare da gargadin jami’an tsaron kasar, kodayake sun bayyana cewa zasu gudanar da zanga-zangar cikin lumana da kwanciyar hankali don juyayin ‘yan kasar uku da suka rasa rayukansu a zanga-zangar da ta gabata.Rehotanni dai na nuna cewa mutane sama da 200,000 ne suka fito domin gudanar da zanga-zangar, inda suka yi cincirindo a daidai babban ginin gwamnatin kasar. 

Al'ummar kasar Albaniya masu gudanar da zanga-zangar adawa da gwamnatin kasar
Al'ummar kasar Albaniya masu gudanar da zanga-zangar adawa da gwamnatin kasar (Photo : Reuters)
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.