Isa ga babban shafi
Faransa-Turkiya-Armenia

Shugaban Faransa Sarkozy ya nemi mutunta juna da Turkiya

Shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy ya nemi a mutunta juna tsakanin kasar shi da Turkiya, a daidai lokacin da ake ci gaba da cacar baki kan aiyana kisan kare dangin Armeniyawa a matsayin laifi da kasar ta Faransa ta yi. 

Shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy
Shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy REUTERS/Jacky Naegelen
Talla

Ya ce ya amince da ra’ayin kasar Turkiya a matsayin ta na aminiyar Faransa kuma muhimmiyar kasa wayaya, amma Faransa ma na fatan ganin an mutunta ta.

Karamar Majalisar dokokin kasar Faransa ta amince da ayar dotar da tabbatar da cewa Turkuya ta yi wa Armeniyawa kisan kare dangi yayin yakin Duniya na Farko, matakin da ya fusata mahukuntan Turkiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.