Isa ga babban shafi
Faransa-Turkiya

Turkiya ta la’anci dokar kisan kiyashin Armeniya a Faransa

Gwamnatin kasar Turkiya ta yi Tir da Allah waddai da dokar da Majalisar Dattawan kasar Faransa suka amince na hukunta duk wani da ya nemi musanta kisan Armeniyawa a zamanin mulkin Othman na Turkiya.

Ministan harakokin wajen kasar Turkiya Ahmet Davutoglu a lokacin da yake bayyana matakan da Turkiya zata dauka akan Faransa
Ministan harakokin wajen kasar Turkiya Ahmet Davutoglu a lokacin da yake bayyana matakan da Turkiya zata dauka akan Faransa Reuters/Umit Bektas
Talla

A jiya Litinin ne Majalisar Dattawan Faransa ta amince da dokar hukunta duk wani mutum, wanda ya musanta kisan kiyashin da Turkiya ta yi wa Armenia a shekarar1915.

Yan Majalisu 86 daga cikin 127 suka amince da dokar, wanda ta tanadi hukuncin daurin shekara guda ga duk wanda yace Turkiya bata aikata laifin ba, da kuma tarar kudi Euro 45,000.

Kasar Turkiya ta bayyana dokar a matsayin rashin hankali, yayin da take cewa, zata dauki kwararan matakai kan Faransa a nan gaba.

A baya dai gwamnatin Turkiya ta janye jekadanta daga kasar Faransa bayan da karamar Majalisar kasar ta amince da sabuwar dokar kafin mayar da shi domin daukar matakan hana majalisar Dattawa amincewa da dokar.

A yau Talata ne kuma ake sa ran Fira Ministan kasar Turkiya, Recep Tayyip Erdogan zai bayyana matakan da zasu dauka akan Faransa a gaban Majalisar Turkiya.

Ana dai zargin kasar Turkiya da kisan Armeniyawa 1915 a zamanin mulkin Othman wanda aka danganta da aikata laifukan yaki.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.