Isa ga babban shafi
Faransa

Shugaban Faransa ya bada umurnin rubuta sabuwar doka kan yiwa Armeniya kisan gilla

Shugaban kasar Faransa, Nicolas Sarkozy, ya bada umurnin rubuta wata sabuwar doka da zata hukunta duk wani mutum da ya musanta kisan kiyashin da aka yiwa Armeniya, bayan kotun fassara kundin tsarin mulki ta yi watsi da dokar da Majalisun kasar suka amince da ita.Fadar shugaban ta bayyana bacin ranta da hukuncin kotun, inda ta ce ba zata amince da musanta kisan kiyashin da Turkiya ta yi na Armeniyawan ba. Kasar ta Turkiya ta yaba da hukuncin kotun.

Shuagaban Faransa Nicolas Sarkozy
Shuagaban Faransa Nicolas Sarkozy REUTERS/Pascal Rossignol
Talla

Wata Babbar Kotun kasar ta Faransa ta haramta dokar da Gwamnatin Shugaba Nicolas Sarkozy ta amince da ita game da hukunta duk wanda ya musanta batun kisan kiyashi da Turkiyya tayi wa Armaniyawa a zamanin yakin duniya.

Babbar Kotun dai ta ce dokar ta sabawa kundin tsarin mulkin kasar Faransa da kuma ‘yancin fadin albarkacin baki na jama'a.

Tuni dai kasar Turkiyya ta yi marhabin da wannan hukunci da kotun Faransan ta yanke, amma kuma Shugaba Nicolas Sarkozy wanda jamiyyarsa ta hakkake sai an kafa dokar sun lashi takobin yin kwaskwarima domin a sake gabatar da dokar, duk da cewa hakan da suka yi da fari ya bata dangantaka matuka tsakanin kasar Faransa da kuma kasar Turkiya.

Kasar Armeniya ta ce akwai mutane da suka kai miliyan 1 ½ da aka kashe tsakanmin shekara ta 1915-16 karkashin mulkin daular Turkiya.

Ita kuwa kasar Turkiya ta ce karya ce mutane kusan dubu 500 suka mutu lokacin yakin.

Faransa dai ta amince da dokar data kafa, dake neman aci taran kudi Euro dubu 45 ko dauri, amman kuma da wannan sabon hukunci da kotu ta yanke, ya warware wancan dokar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.