Isa ga babban shafi
Amurka-Ireland

An halasta zubar da Ciki domin ceto rayuwar Mata a kasar Ireland

Zubar da ciki domin ceton Rai na mahaifiya dan-Tayi a kasar Ireland ya halarta muddun akwai hujjar yin hakan, kuma zai ceci rayuwarta, shugaba kasar Micheal D Higgins ne ya rattaba Hannu kan wannan dokar a jiya da ta janyo rabuwar kawunan mabiya cocin katolika a kasar

Wata mata a kasar Irelan dauke da rubutaccen sako
Wata mata a kasar Irelan dauke da rubutaccen sako REUTERS/CATHAL MCNAUGHTON
Talla

Mahunkunta a kasar sun sanya hannun kan wannan dokar a farkon watan yuli sanadiyar cece-ku-ce da ya biyo bayan mutuwar wata mata ‘yar kasar India da ta rasa ranta a kasar ta Ireland bayan da likitoci suka ki amincewa da cire mata jaririn da ya yi sanadiyar rasuwarta.

Mataimakin Piraiministan kasar Eamon Gilmore ya ce wannan dokar na da mahimmanci kwarai mussaman ga matan Ireland, inda ya kara da cewa makasudin wannan dokar dai shi ne taimakawa domin ceto rayuwar mata da kuma kare hakkinsu.

Dokar ta kawo karshen sa-in-sar da ake kan lamarin a Ireland bayan wani hukunci na kotun kare hakin bil’adama a shekara ta 2010 inda ta sami kasar Ireland da kin sanya dokar zubar da cikin dokokinta, musamman ma yayin da mace ke fuskantar barazana rasa ranta lokacinda take dauke da juna biyu.

Akalla mata 4000 ne a shekarar da ta gabata suka bar kasar ta Ireland zuwa kasar Ingila da kuma Wales domin zubar da ciki kamar yadda hukumar lafiya ta Britainiya ta sanar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.