An cafke Gerry Adams
Gwamnatocin Birtaniya da Ireland sun musanta zargin Cafke Gerry Adams yana da nasaba da Siyasa, wanda ke amsa tambayoyi a hannun ‘Yan sandan Arewacin Ireland. A ranar Laraba ne aka Cafke Shugaban na Sinn Fein akan tuhumarsa da laifin kisa a shekarar 1976.
Wallafawa ranar:
Mista Adams mai shekaru 65 tuni ya yi watsi da zargin kisan tarr da danganta al’amarin da siyasa.
Ana zargin Adams ne laifin kisan Jean McConville da aka kashe bayan sace ta daga gidanta.
Sinn Fain da Mista Adam ya jagoranta, Jam’iyyar siyasa ce da ta kaddamar da yaki a Arewacin Ireland domin shiga ikon Ireland, a yayin da shugabanninta ke zargin Gwamnatocin Birtaniya da Ireland da kokarin karya ayyukansu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu