Isa ga babban shafi
Faransa

An haifi ‘yayan Damisar Sri Lanka a Faransa

A gidan ajiyar Namun daji a kasar Faransa an haifi wasu ‘yayan damisa ‘Yan asalin kasar Sri Lanka, inda yanzu adadin yawansu ya karu bayan an bayyana kimanin 700 suka rage a dawa.

Damisar Sri Lanka
Damisar Sri Lanka Wikipedia
Talla

An haifi ‘Yayan Damisar ne guda biyu a gidan ajiyar namun daji a arewacin Faransa, kuma wannan shi ne ya kara yawan na’uin damisar asalin kasar Sri lanka, inda yanzu kimanin 700 ne aka ce sun rage a daji, kamar yadda Jami’an gidan namun dajin a Faransa suka tabbatar.

Ana kiran Damisar ne a kasar Sri lanka da sunan Kotiya a lardin Tamil. Kuma kungiyar da ke nazarin kalubale na muhalli a duniya tace Damisar Sri Lanka tana da matukar hadari, amma sun ragu ne saboda barazana ta lalata gandun daji.

Kimanin nau’in Damisar Sri Lanka 60 ne yanzu ake tsare da su a gidajen namun daji a sassan kasashen Turai

A ranar 1 ga watan Yuli ne aka haifi ‘yayan damisar na Sri Lanka guda biyu a wani gidan namun daji mai dauke da dabbobin dawa kimanin 300 da ke kan iyaka da kasar Belgium a kasar Faransa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.