Isa ga babban shafi
Faransa

Kotun Faransa ta bukaci a gurfanar da Lagarde

Bayan share tsawon shekaru biyu ana gudanar da bincike a kanta, a yanzu dai kotun kasar Faransa, ta bukaci a gurfanar da shugabar asusun lamuni na duniya IMF Christine Lagarde a gaban kotu, domin cajinta da laifin rashawa a lokacin da ta ke rike da mukamin Ministan tattalin arzikin kasar shekaru 6 da suka gabata.

Christine Lagarde shugabar asusun lamuni na duniya IMF
Christine Lagarde shugabar asusun lamuni na duniya IMF REUTERS/Philippe Wojazer/Files
Talla

Shugabar Asusun Lamanin na Duniya, ta tabbatar wa manema labarai cewa tuni aka sanar da ita wannan matsayi da kotun ta Faransa ta dauka, sai dai ta ce ba za ta yi marabus daga mukaminta saboda wannan batu ba.

Ana dai zargin Christine Lagarde ne da tsoma baki domin ganin cewa an bai wa wani dan kasuwar kasar mai suna Bernard Tapie da kuma wani bankin kasar, damar samun kwangila a Faransa.

A yanzu dai hankulan sun karkata zuwa ga Majalisar gudanarwar ta asusun lamanin na duniya domin fayyace makomar Lagarde, wato ci gaba da rike mukaminta ko kuma tube ta domin bai wa bangaren shari’ar damar ci gaba da aikinsa.

Zargin da ake yi wa Christine Lagarde ya samo asali ne tun a shekara ta 2008 lokacin da take rike da mukamin ministan tattalin arzikin Faransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.