Isa ga babban shafi
Ireland

Tsarin auren jinsi guda ya samu shiga a ireland

A yau assabar kasar Ireland ta amince da tsarin auren jinsi guda, bayan masu na’am da tsarin sun samu rinjaye a kuri’ar jin ra’ayi da aka kada a jiya juma’a, da kashi sama da 62 cikin dari na yawan kuri’un da aka jefa.Tuni daruruwan masu na'am da wannan tsarin suka bazama a kewayen kasar domin murnar farin cikinsu.

Masu Murna da tsarin auren Jinsi daya a Ireland
Masu Murna da tsarin auren Jinsi daya a Ireland REUTERS/Cathal McNaughton
Talla

Gwamnatin kasar Ireland ta bayyana cewar, wannan sakamakon ya nuna cewa kasar su za ta zamto kasa ta farko a Nahiyar Turai, da kuri'ar jin ra’ayi zai ba ta damar kafa dokar auren jinsi guda, bayan masu adawa da tsari kashi 38 kawai garesu a cikin 100.

A cikin shekarar ta 1993, dokar kasar Ireland ta haramta wannan tsari na auren jinsi daya, da kuma zub da ciki da gan-gan, lamari da bai dadawa masu ra'ayin auren jinsi daya ba.

A yanzu dai Ireland ita ce kasa ta 19 a duniya data amince da tsarin auren jinsi guda,kuma ta 14 a Nahiyar turai.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.