Isa ga babban shafi
Faransa

Bafaranshiyar da aka yi garkuwa da ita a Yemen ta isa Faransa

Bafaranshiya mai suna Isabelle Prime da aka saka bayan anyi garkuwa da ita a Yemen kusan watanni shida, ta isa Faransa.

Bafaranshiya Isabelle Prme
Bafaranshiya Isabelle Prme Ayala Consulting
Talla

Tuni dai Ministan harkokin wajen kasar Laurent Fabius ya ce sako Isabelle ya kara bayyana cewa Faransa ba ta sakaci wajen daukan dawainiya da ya zame mata wajibi.

A ranar 24 ga watan Fabairun bana ne aka yi garkuwa da Isabella Prime mai shkekaru 30 a kasar ta Yemen.

Gabanin isowar ta asalin kasar ta, Isabelle ta kasance karkashin kulawar jami’an Faransa da ke Yemen bayan sakin ta, inda kuma daga nan ta isa Oman.

An dai kama Isabella wadda ke aiki da Bankin Duniya tare da mai mata fassara ne a birnin Sanaa, amma daga bisani an saki abokin aikinta a watan Maris din daya gabata.

Babu dai wani bayani kan wadanda suka yi garkuwa da ita, amma a watan Yuni an nuna ta a wani hoton bidiyo na You Tube.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.