Isa ga babban shafi
Hungary

Hungary ta bude tashar jirginta saboda bakin haure

Daruruwan ‘Yan gudun hijira sun yi cincirindo a babban tashar jirgin kasa ta Kasar Hungary bayan Jami’an ‘Yan Sanda sun sake bude tashar a safiyar yau Alhamis.

'Yan gudun hijira kusan dubu 150 suka shiga Hunagary a cikin wannan shekarar ta 2015.
'Yan gudun hijira kusan dubu 150 suka shiga Hunagary a cikin wannan shekarar ta 2015. REUTERS/Leonhard Foeger
Talla

Da misalin karfe takwas agogon Kasar ne Jami’an ‘Yan Sandan suka bude babbar kofar shiga cikin tashar jirgin yayin da ‘Yan gudun hijiran suka yi ta turereniya tare da fada da juna a yunkurinsu na samun damar shiga cikin wani jirgin Kasa da ya shirya tafiya zuwa birnin Sopron dake kusa da kan iyakar Kasar Austria.

To sai dai Kamfanin jiragen Kasar Hungary ya sanar cewa Jirgin ya fasa tafiya kuma babu wani jirgi da zai bar tashar ta Keleti da nufin shiga Kasashen yammacin Turai har nanda wani loakci.

Kasar Hungary dai wata hanya ce da ke baiwa dubban ‘Yan gudun hijira damar kutsawa kasasahen Turai yayin da sama da ‘Yan gudun hijira dubu 50 suka shiga kasar a cikin watan Agustan daya gabata kadai.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.