Isa ga babban shafi
Ukraine-MDD

Kusan mutane 8,000 ne suka rasa ransu a rikicin kasar Ukraine

Wani rahoton hukumar kare hakin dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar yace, kusan mutane 8,000 ne suka rasa rayukansu, tun bayan barkewar rikicin kasar Ukraine cikin shekarar bara. Rahoton ya kuma kara da cewa wasu mutanen sama da dubu goma sha bakwai sun sami raunuka sakamakon rikicn.  

Mambobin kwamitin tsaro na MDD, a lokacin wani zama muhawara
Mambobin kwamitin tsaro na MDD, a lokacin wani zama muhawara Reuters/路透社
Talla

Rikicin gabashin Ukraine, da ya soma a watan Afrilun bara, ya kara kazancewa sakamakon yawan mutanen da suke mutuwa wadanda yawancin su fararren hula ne, abinda hukumar kare hakin dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana a matsayin abin damuwa ganin yadda ake ci gaba da samun yawan mace macen fararren hula da basu ji ba basu gani ba.

Majalisar ta ce abin damuwa game da rikicin shine yadda aka samu karuwar wadanan alkaluma a tsakanin watan Mayu da Augusta wannan shekarar.

Batun samar da yarjejeniyar zaman lafiya mai dorewa a kasar Ukraine dai ya gagara, sai dai kuma a karon farko an dauki tsawon mako guda ba tare da rikici a tsakanin bangarorin biyu dake fada da juna ba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.