rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Ireland

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Firaministan Ireland ya yi barazanar Murabus

media
Taswirar kasar Ireland www.lonelyplanet.com

Firaministan kasar Irelande ta arewa mai ra’ayin kwadago Peter Robinson ya yi barazanar yin murabus daga kan mukaminsa idan har majalisar dokokin yankin ba ta fasa ko jingine mahawarar baya-bayan nan da ta tanadi Rusa rundunar sojan jamhuriyar Ireland ta arewa ba.


Kwamitin Majalisar dokokin da ke kula da tsara maudu’in da majalisar dokokin yankin mai cin kwarya-kwaryar gashin kai daga kasar Britaniya, a yau alhamis ne, ya kamata ya tattauna bukatar da Firaministan ya gabatar kan jingine maganar.

A cewar Robinson wannan batu ba karamin barazanar ya ke haifarwa ba ga ci gaban zaman lafiyan kasar.