Isa ga babban shafi
EU-Hungary

Hungary za ta hukunta Bakin haure 367 da suka saba doka

‘Yan sandan Hungary sun cafke kimanin bakin haure 367 da suka saba sabuwar dokar da kasar ta kafa kan matakan shiga kasar ta barauniyar hanya bayan sun tsallaka katangar waya kan iyaka da Serbia.

Hungary za ta hukunta Bakin haure 316 da suka saba sabuwar dokar shiga kasar
Hungary za ta hukunta Bakin haure 316 da suka saba sabuwar dokar shiga kasar REUTERS/Laszlo Balogh
Talla

‘Yan sanda Hungary sun ce za su hukunta bakin haure 316 da suka lalata shingen wayar da aka kafa akan iyakar kasar da Serbia. Kuma 51 daga cikinsu za su fuskanci hukunci na shiga kasar ta barauniyar hanya.

Hungary ta ce adadin bakin haure 9,380 ne suka tsallaka kasar wadanda ke neman shiga kasar Jamus.

Hungary ta rufe kan iyakarta da Serbia ne da nufin hana sabbin baki shiga Kasar.

Dubban bakin haure ne dai ke ci gaba da kwarara zuwa Turai, yawancinsu mutanen Syria da ke gujewa rikicin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.