rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Portugal

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

'Yan adawa sun tsige gwamnatin Portugal

media
Firaministan portugal da aka tsige gwamnatinsa, Pedro Passos Coelho. REUTERS/Rafael Marchante

Kawancen jam’iyyun adawar kasar Portugal ya tsige gwamnatin Firaminista Pedro Passos Coelho kasa da makwanni biyu da hawa karagar mulki.


‘Yan adawar da suka kunshi 'yan Jam’iyyun Socialists da Communists da kuma kawayensu, sun kada kuri’ar rashin amince wa da shirin gwamnatin wanda ya nuna faduwar gwamnatin gaba daya.

Wannnan ita ce gwamnati mafi karancin rayuwa a tarihin kasar tun komawar Portugal mulkin demokiradiya a shekarar 1974.

A watan jiya ne kawancen jam’iyyun Firaministan kasar ya lashe akasarin kuri’un da aka kada a zaben da aka gudanar amma ya rasa samun rinjayen da ya ke da shi a majalisa tun shekara ta 2011.