rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Auren jinsi Ireland

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Dokar amincewa da auren jinsi ta fara aiki a Ireland

media
Mabiya Darikar Katolika na adawa da auren jinsi guda a Turai REUTERS/Nate Chute

Dokar amincewa da auran jinsi guda zata fara aiki a kasar Ireland a yau Litinin watanni shida bayan al’ummar kasar sun kada kuri’ar amincewa da dokar.


Dokar za ta amince da duk wadanda suka kulla auran jinsi guda a waje sannan dokar ta ba sabbin masu bukatar auren su gabatar da bukatarsu.

Masu bukatar auren za su mika bukatunsu watanni kafin ranar daura aure, karkashin dokar a Ireland.

Kashi sama da 62 na masu zabe ne suka amince da dokar ta auren jinsi guda, wanda wannan ya sabawa karantarwar mabiya darikar Katolika a kasar.