rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya
Gaggauce
Kotun Kolin Najeriya ta tabbatar da nasarar Ganduje a matsayin gwamnan Kano

Tarayyar Turai David Cameron Bakin-haure

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

EU na sake nazarta hanyoyin samar da mafita ga matsalar kwararar bakin haure a yankunansu

media
Tutar EU a sansanin 'yan gudun hijra dake Slovenia REUTERS/Antonio Bronic

A yau alhamis Shuwagabannin kasashen Turai sun hallara a birnin Bruxelles na kasar Belgium, domin sake nazarta hanyoyin samar da mafita ga matsalar kwararar bakin haure a cikin kasashensu.


Yan awowi bayan buda babban zaman taron na yau shugaban Kwamitin zartarwar kungiyar tarayyar Turai Jean-Claude Juncker, ya shaidawa manema labarai cewa, manufar taron ita ce ganin kasashen na turai sun dauki tsauraran matakai na bai daya, da za su kawo karshen matsalar kwararar yan gudun hijira da bakin haure a cikin kasashen nasu.

A jiya talata ma dai Mr Juncker ya bukaci kasashe mambobin kungiyar tarayyar Turan da su goyi bayan shawarar da ya gabatar ta bukatar kafa wata babbar rundunar tsaron kan iyakokin kasashensu.

Shirin da kungiyar ta Turai ta danganta da mai matukar muhimmanci da ya tanadi yiyiwar amfani da rundunar a wata kasa da ta baude, shawarar da kasashe irin su Girka ta nuna dari darin sallada wani sashen ikonta ga ‘yan bani na iya.

Wannan zaman taro dai na bukatar ganin kasashen na turai sun kara matsa kaimi wajen magance matsalar bakin haure da ta dauki sabon salon da ke gab da jefa nahiyar Turai cikin matsalar kwararar bakin haure mafi muni da aka taba gani a tarihinta A yayin da PM Britaniya David Cameron ke Barazanar fitar da kasarsa daga cikin kungiyar tarayyar turan idan ba a duba wasu bukatun da ya gabatar ba.

A lokacin da yake bashi amsa shugaban Faransa Francois Hollande yace ba za ta taba yiyiwa ba a sake fasalta yarjejeniyar da ta kafa kungiyar tarayyar turai kamar yadda David Cameron da zai aika yan kasar a rumfunan zaben raba gardamar ficewar kasar a kungiyar tarayyar Turai ke bukata.