Isa ga babban shafi
Slovenia

‘Yan Slovenia sun ki amincewa da auren jinsi guda

Masu kada kuri’a a kasar Slovenia sun ki amincewa da bukatar halatta auran jinsi guda a fadin kasar bayan sakamakon zaben raba gardama ya nuna cewar sama da kashi 63 na masu zaben sun yi watsi da bukatar.

'Yan Slovenia sun kada kuri'ar kin amincewa da auren jinsi guda
'Yan Slovenia sun kada kuri'ar kin amincewa da auren jinsi guda JURE MAKOVEC / AFP
Talla

Sakamakon zaben raba gardamar da aka gudanar a ranar Lahadi a Slovenia mai yawan mabiya darikar Katolika ya nuna gagarumar koma baya ga masu rajin kare hakkin masu auran jinsi guda.

Sama da kashi 63 na masu zaben suka shure bukatar Majalisar na mayar da aure tsakanin mutane biyu maimakon mace da na miji.

Wata kungiyar da ke fafutukar ganin an ci gaba da haihuwa a kasar ta samu sanya hannun mutane 40,000 da ke adawa da auren.

Yanzu haka dai kasashe 18 suka amince da auran jinsi guda a duniya, kuma 13 daga cikinsu suna nahiyar Turai.

Kasashen sun hada da Holland da Belguim da Spain da Norway da Sweden da Portugal da Iceland da Denmark da Faransa da Ingila da Ireland da Luxembourg da Finland.

A nahiyar Amurka akwai kasashen Amurka da Canada da Mexico da Argentina da Uruguay da Brazil.

Afirka ta kudu kadai a nahiyar Afirka ta amince da auren jinsi guda sai kuma New Zealand a Asia.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.