Isa ga babban shafi
Canada

Canada ta kawo karshen hare-hare akan ISIL a Syria da Iraki

Canada ta sanar da kawo karshen hare haren da ta ke kaiwa akan ‘yan kungiyar ISIL a Iraqi da Syria, ta kuma ce zata dawo da jiragen yakin ta 6 gida a ranar 22 ga watan Nuwanba.

Firaiyi ministan kasar Canada Justin Trudeau
Firaiyi ministan kasar Canada Justin Trudeau REUTERS/Chris Wattie
Talla

Sanarwar dai ta gamu da suka daga al’ummar kasar ganin yadda suke sukar wannan manufar, a  kuri’ar jin ra’ayin jama’a na baya bayan nan, galibin jama’ar Canadan na goyon bayan ci gaba da kaiwa kungiyar ISIL hare hare, lura da yadda wasu hare haren kungiyar a kasashen Burkina faso da birnin Jakarta suka hallaka ‘yan kasar 6.

Firaiyi ministan kasar Mr Justin Trudeau, ya ce ya tuntunbi shugaban Amurka Barack Obama da safiyar yau kuma sun tattauna makomar kasar game da ci gaba da kaiwa kungiyar ta ISIL hare hare, kuma ya gamsu da amfanin Canada kan rawar da muke takawa a wannan yaki da ake.

To sai dai Mr Trudeau yace nan bada jimawa ba ne zasu fitar da matsayin Canada na hakika lura da halin da’ake ciki na masassarar tattalin Arziki, idan aka ga abunda kasar ke kashewa a wannan yaki.

A hannu daya kuma rikicin Syria na kara kazanta, al’amarin da ke kara yawaitan ‘yan gudun hijirar kasar dake kwarara akan iyakokin kasashen Duniya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.