Isa ga babban shafi
Belarus-EU

Kasashen Turai sun janye wa Belarus takunkumi

Kungiyar Tarayyar Turai ta bayyana dage takunkuman da ta dora kan wasu shuwagabannin kasar Belarus 170 da ta kakaba masu domin kara masu kwarin guiwar ci gaba da mutunta tsarin hakkin dan adam a kasar.

Shugaban Belarus Alexandre Loukachenko
Shugaban Belarus Alexandre Loukachenko AFP/BELTA POOL/AFP
Talla

Mutanen sun hada da shugaban kasar Alexandre Loukachenko

Ministocin harakokin wajen kasashen kungiyar ta Tarayyar turai 28 ne da suka gudanar da zaman taron su a ranar Litinin a Bruxelles na kasar Belgique inda suka amince da kudirin da ya bayar da damar sauke takunkuman da ya hada da wasu kamfanoni uku.

Sai dai ba dukkanin takunkuman akan kasar Belarus ba aka dage.

An kakabawa Belarus Takunkuman hana sayar da da makamai da wadanda aka dora akan wasu manyan mutane dangane da kisan da aka yi wa wasu mutane biyu da aka kasa samun haske a kai.

Mutanen da aka kashe sun hada ne, da wani dan kasuwa guda da dan jarida.

Babbar jami’ar diflomasiyar kungiyar Turai Federica Mogherini ta ce an sassautawa kasar Belarus takunkuman ne ganin ta dan soma inganta tsarin kare hakkin dan adam a kasar, domin kara mata kwarin guiwar ci gaba da bin tafarkin, duk da cewa ba gaba daya aka gamsu da yadda kasar ke tafiya ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.