Isa ga babban shafi
Girka

Masu taimaka wa 'yan gudun hijirar Girka sun fice

Wasu karin kungiyoyin agaji da su ke taimaka wa 'yan gudun hijirar da ke Girka sun fice daga kasar saboda abinda suka kira yadda aka mayar da sansanin wurin tsare mutane.

'Yan gudun hijira na cikin tsaka mai wuya
'Yan gudun hijira na cikin tsaka mai wuya
Talla

Wannan na zuwa ne bayan janyewar hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya.

Su dai wadannan kungiyoyin agaji sun ki amincewa ne da yarjejeniyar da kungiyar kasashen Turai ta kulla da kasar Turkiya wajen gaggauta rajistar bakin da kuma duba bukatarsu ta mafaka, abinda ya kai ga tsare daruruwan su da suka isa Girka.

Bisa ka’ida duk wanda aka ki amincewa da bukatarsa za a mayar da shi ne kasar Turkiya.

Su dai wadannan kungiyoyi sun ce, hada kai da kasar Girka wajen tsare bakin zai zama wani goyan baya ne ga yadda kasar ke cin zarafin bakin.

Kungiyoyin agaji biyu sun bayyana cewar za su bi sahun hukumar 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar Medicins Sans Frontier don janyewa daga Girka.

Ita kuwa kakakin kungiyar agaji ta International Rescue Committee, Lucy Carrigan cewa ta yi, jami’anta ba za su sake dibar bakin suna kai wa inda za a tauye musu hakkokin su ba.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.