rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya
Gaggauce
Kotun Kolin Najeriya ta tabbatar da nasarar Ganduje a matsayin gwamnan Kano

Ingila David Cameron Panama

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Cameron ya amsa fallasar Panama

media
Friministan Britaniya David Cameron REUTERS/Stefan Wermuth

Firaministan Birataniya David Cameron ya ce ko shakka babu ya taba amfana da kudaden da ake cewa mahaifinsa ya mallaka a kasashen ketare kamar dai yadda bayanan sirri na Panama da aka fallasa suka ambaci sunansa.


Bayan share tsawon kwanaki hudu ba tare da ya ce uffan a game da wannan zargi ba, daga bisani Cameron ya tabbatar da cewa ya gaji hannayen jari wadanda ya sayar a shekara ta 2010 da kimarsu ta kai Euro dubu 40.

Zargin rashawa ko kuma boye kudade a kasashen ketare, ya shafi shugabannin kasashen duniya da dama da suka hada da Mauricio Macri na Argentina, da shugaban Rasha vladimir Putin har ma da shugaban China Xi Jinping da dai sauransu.

A halin yanzu dai Shugaban Argentina na fuskantar bincike a game da zargin rashawa.