rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya
Gaggauce
Kotun Kolin Najeriya ta tabbatar da nasarar Ganduje a matsayin gwamnan Kano

Ingila David Cameron

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Camaron ya sha Suka daga Jam’iyyar Labour kan Sadiq Khan

media
Friministan Britaniya David Cameron REUTERS/Christopher Furlong/Pool

Magoyo bayan Jam’iyyar Labour a Birtaniya sun yiwa Firaminista David Cameron ca, kan kalamun batunci da ya yi akan takarar kujerar Magajin Garin birnin London Sadiq Khan, inda ya zarge shi da alaka da mai goyan bayan kungiyar ISIS.


Cameron yayin jawabin ne a zauren Majalisa ya zargi dan takaran Khan da alaka da wani limami da ake kira Sulaiman Ghani wanda ake zargin yana goyan bayan ayyukan ta’addanci.

'Yan Majalisa daga Jam’iyyar Labour a zauran Majalisar sun yiwa Firaministan ihu inda suka kira shi mai nuna bambamcin launin fata, inda shugaban su Jeremy Corbyn ya bayyana kalaman Cameron a matsayin abin kunya, wanda ya dakushe kimar ofishin Firaminista.

Khan wanda tsohon minista ne kuma dan assalin kasar Pakistan, na sahun gaba wajen shirin lashe zaben kasar da za’ayi a watan Mayu.