Isa ga babban shafi
Auren Jinsi

Ranar yaki da masu kyamar auren jinsi

Yau ce ranar nuna adawa ga masu kyamar ‘yan luwadi da madigo a duniya, duk da cewa wasu daga cikin al’ummar Duniya na ci gaba da caccakar tsarin, ganin ya sabawa al’adarsu da addini.

Auren jinsi guda a Taiwan
Auren jinsi guda a Taiwan Reuters
Talla

Bikin na yau na zuwa ne a dai dai lokacin da wasu daga cikin mabiya addinan Islama da Kirsta ke ci gaba da yin tir da ‘yan luwadin da madigo har ma da masu auren jinsi guda da kuma ‘yan daudu, da matan da ke sauya halittarsu don kama da maza, ko kuma maza da ke yin haka don kama da mata.

A karo na 12 kenan da ake gudanar da irin wannan biki na nuna kyama ga ‘yan luwadin, yayin da masu goyon bayan tsarin suka yi ta yada hotuna a shafukan intanet da ke nuna namiji na simbatar dan uwansa namiji da kuma macen dake sinbatar ‘yar uwarta.

To sai dai a wannan ranar, wasu kasashen kamar Afrika ta kudu sun mayar da hankali ne kan wayar da kan ‘yan luwadin dangane da yadda yakamata su rika saduwa da juna domin kaucewa kamuwa da cututtuka.

A Afrika ta kudu dai, akwai kimanin mutane miliyan 4.9 da ke tutuyar cewa, su yan luwadi ne kuma basa kunyar bayyana hakan a bainan jama’a.

Kungiyoyin kare hakkin dan adam dai na ganin cewa, duk wani dan adam na da damar gudanar da rayuwarsa yadda yake so kuma sun yi allawadai da matakan nuna kyama ga ‘yan luwadin da madigo.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.