rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya
Gaggauce
Kotun Kolin Najeriya ta tabbatar da nasarar Ganduje a matsayin gwamnan Kano

Birtaniya Tarayyar Turai David Cameron

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Birtaniya: Cameron ya mika mulki ga Theresa May

media
Sarauniyar Ingila tare da Sabuwar Firaministan Birtaniya Theresa May a Fadar Buckingham a London REUTERS

David Cameron ya mika ragamar tafiyar da mulki ga Tharesa May wacce aka rantsar a matsayin sabuwar Firaministan Birtaniya, bayan Sarauniyar Ingila ta amince da murabus Cameron a yau Laraba.


Sarauniyar Ingila Elizabeth ta biyu ta bukaci sabuwar Firaministar ta gaggauta kafa gwamnati.

Cameron ya yi murabus ne bayan rashin samun nasara a kuri’ar raba gardama da aka kada a ranar 23 ga watan Yuni kan ficewar Birtaniya a Kungiyar Tarayyar Turai.

A lokacin da ya ke jawabin ban kwana a kofar ofishin Firaminista a Downing Street a London, Cameron ya amsa fuskantar kalubale bayan shafe shekaru 6 yana Firaminista.

Cameron ya yi wa Birtaniya fatan alheri bayan ya fice Downing Street tare da iyalan shi.

Tharesa May dai ta rike Ministan cikin gida a gwamnatin David Cameron, amma babban kalubalen da ke gabanta a yanzu shi ne kare muradun Birtaniya a tattaunawar da za ta jagoranta da Tarayyar Turai kan batun ficewar kasar a Kungiyar.