Isa ga babban shafi
Japan

Shekaru 71 da kai kazamin harin bam mai guba

Yau birnin Nagasaki dake kasar Japan ke cika shekaru 71 da kazamin harin bam mai guba da Amurka ta kai wanda ya lalata garin, bayan hallaka mutane sama da 74,000.

Shugaba Shinzo Abe na kasar Japan a ranar nuna alhini kan kisan dubban mutane a birnin Nagasaki
Shugaba Shinzo Abe na kasar Japan a ranar nuna alhini kan kisan dubban mutane a birnin Nagasaki REUTERS/Toru Hanai
Talla

Za’a soma tuna ranar da kada kararrawa da misalin karfe 11 da mintina 2 na kasar a gaban dubban mutane, wanda yayi dai dai da lokacin da Amurka ta jefa bam din.

Harin na Nagasaki na zuwa ne kwanaki uku bayan Amurka ta jefa wani bam irin wannan a Hiroshima wanda ya kashe mutane 140,000.

Magajin Garin birnin Tomihisa Taue yace ya yaba da ziyarar da shugaba Barack Obama ya kai kasar wadda itace ta farko da wani shugaban Amurka ya kai kasar tun bayan aukuwar al’amarin da ya kasance karon farko da ake anfani da makami mai guba akan dan adam.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.