rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Portugal Spain Faransa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Ana kokarin kashe gobarar daji a Turai

media
Wutar daji dazukan Faransa

Jami’an kashe gobora sun ce suna samun nasara a kokarin da suke na shawo kan wutar daji data mamaye yankuna masu fadi a dazukan Portugal da Faransa.


Sai dai sanarwar na zuwa ne daidai lokacin da kasar Spain ke bayyana fargabar ta, kan yiwuwar gobarar dajin ta shafi wasu sassa a yankin arewa maso yammacin kasar.

Wutar data mamaye arewacin Portugal da wani tsibiri, ta yi sanadin rasa rayukan mutane 3 a cikin wannan makon.

A wannan shekara dai wasu kasashe a yankin turai sun sha fama da gobarar daji wadda ta yi sanadin raba daruruwan mutane da gidajensu tare da rasa rayuka.