rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Portugal Spain

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Gobara ta kone abincin dabbobi a Gandun Daji

media
Wutar daji a Portugal ta tilastawa mutane ficewa daga gidajensu REUTERS/Patrick T Fallon

Dubban masu kashe gobara daga kasashen Spain da Portugal suna cigaba da kokarin shawo kan wata gagarumar wutar daji da ta tashi a kusa da Gandun Dajin Peneda-Geres dake kasar Portugal kusa da iyakarta da Spain.


Wutar dajin da ta zama daya daga cikin mafi muni da aka taba gani a yankin ta tilastawa mazauna wurin barin gidajensu.

Magajin garin Arcos de Valdeves, Helder Barros da ke kusa da Gandun Dajin na Peneda-Geres, ya ce wutar dajin ta kone kusan baki dayan abincin da dabbobin wurin, ciki harda ciyawar da ke shuke a Gandun dominsu.

Kimanin masu kashe gobara 2,700 aka tura domin kashe gobarar dajin.