rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya
Gaggauce
Kotun Kolin Najeriya ta tabbatar da nasarar Ganduje a matsayin gwamnan Kano

Ingila David Cameron Tarayyar Turai

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Cameron ya yi murabus daga majalisar dokokin Britaniya

media
David Cameron ya sanar da yin murabus daga majalisar dokokin kasar Britaniya Parliament TV/Handout via REUTERS TV

Tsohon Firaiyi Ministan Brittaniya David Cameron ya yi murabus daga mukaminsa na dan majalisar dokoki dake wakiltar mazabarsa ta Witney kamar yadda ya tabbatar a wata sanarwa da ya fidda a jiya Litinin.


David Cameron ya fara yin murabus daga matsayinsa na Firaiminstan Birtaniya a watan Yuni bayan da al’ummar kasar suka zabi ficewa daga tarayyar Turai a zaben raba gardaman da’a aka gudanar a kasar.

Cameron mai shekaru 49 ya wakilci mazabar Witney tun shekarar 2001 kafin ya tsaya takarar kujerar Firaiyi minista karkashin jam’iyyarsa ta Conservative inda ya lashe zaben ya kuma rike mukamin na Firaiyi Minista na tsawon shekaru shida.