Isa ga babban shafi
Mexico

Dubban mutane sun nemi shugaban Mexico yayi murabus

Dubban ‘yan kasar Mexico ne suka gudanar da wata zanga zanga, inda suke bukatar shugaban kasar Enrique Pena Nieto ya sauka daga kujerarsa.  

Masu zanga zangar neman shugaban kasar Mexico Enrique Pena Nieto ya sauka daga kujerarsa
Masu zanga zangar neman shugaban kasar Mexico Enrique Pena Nieto ya sauka daga kujerarsa Fuente: Reuters.
Talla

Shugaban Mexicon ya fara fuskantar wannan tirjiya saboda kasa magnace matsalar safarar miyagun kwayoyi, cin hanci da rashawa da kuma ganawar da yayi da Donald Trump, dan takarar shugabancin Amurka.

Masu zanga zangar sun yi tattaki zuwa Dandalin Zocalo inda shugaban kasar ke tsayawa dan girmama ranar samun yancin kan kasar da akayi a ranar 1810.

Cikin wadanda suka shiga zanga zangar harda iyayen daliban nan 43 da suka bata tun ranar 26 ga watan Satumba na shekarar 2014.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.