Isa ga babban shafi
Amurka

Trump ya gana da Netanyahu

Dan takarar shugabancin kasar Amurka karkashin jam’iyyar Republican Donald Trump, ya gana da Firaministan Isra’ila Benyamin Netanyahu a birnin New York.  

Dan takarar shugabancin Amurka karkashin Jam'iyyar Republican Donald Trump.
Dan takarar shugabancin Amurka karkashin Jam'iyyar Republican Donald Trump. REUTERS/Mike Segar
Talla

Ganawar tasu ta maida hankali kan batutuwan, kokarin murkushe Mayakan ISIS, shirin inganta makamashin Nukiliya da Iran ke yi, sai kuma, batun ginin ganuwar da Isra’ila ke yi tsakaninta da yankin Falasdinawa.

Bayan kamalla taron Trump ya sanar da cewa taimakon soja da Amurka ke bawa Isra’ila abu ne da yake maraba dashi wanda ya ke fatan ya dore.

Dan gane da rikicin falasdinawa da Isra'ila kuma Trump ya ce muddin ana son zaman lafiya tsakanin Isra’ila da Falasdinawa, dole ne Falasdinawan su amince da kafuwar Isra’ila a matsayin kasar Yahudu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.