Isa ga babban shafi
Kimiyya-Turai

Tauraron Rosetta ya tarwatse

A yau ne tauraron na Rosetta wanda aka rika bashi umarni daga birnin Darmstadt na Jamus ya isa duniyar Comet domin tattaro wasu bayanai na musamman game da asalin falakin rana.

Daya daga cikin hotunan da Tauraron Rosetta a aiko daga wajen Duniya
Daya daga cikin hotunan da Tauraron Rosetta a aiko daga wajen Duniya ESA/Rosetta/MPS for OSIRIS Team
Talla

Jim kadan da isarsa duniyar, Rosetta ya ci karo da curin kankara mai hade da kura da iska kamar yadda aka tsara, lamarin da haifar da shewa da tafi tsakanin masu binciken, ganin cewa hakarsu ta cimma ruwa.

Gabanin tarwatsewarsa dai a wajen Duniya da wasu ‘yan sa’o’i, Rosetta ya aiko da wasu hotuna da kuma gwaje-gwajen wani curin kankara mai dauda.

Tauraron wanda aka harba don tattaro bayanai game da asalin duniyar rana, ya yi nasarar dauko wasu hotuna na musamman duk da cewa wasu bayanai sun lalace kamar yadda cibiyar binciken sararin samaniyar ta Turai ta sanar.

Daga cikin masana kimiyan da suka harba tauraron, akwai wadanda suka shafe tsawon shekaru 30 suna aikin domin ganin an harba Rosetta don tattaro bayanan.

Cibiyar binciken sararin samaniyar ta bayyana wannan tafiya ta Roseeta a matsayin wadda ta yi nasara, kuma hakan zai taimaka wajen kara fahimtar yanayin curin kwallayen kankara masu dauda da ke yawo a tsakankanin duniyoyi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.