Isa ga babban shafi
Bakin-Haure-Amnesty

Kasashe masu arziki ba sa taimakawa 'yan gudun hijira inji Amnesty

Kungiyar Kare hakkin Bil Adama ta Amnesty International ta zargi kasashen da suka fi arziki a duniya da kin taimakawa baki 'yan gudun hijira, yayin da ta ke cewa yanzu haka kasashe matalauta 10 ke daukar nauyin kashi 56 na bakin.

Amnesty International ta zargi kasashen da suka fi arziki a duniya da kin taimakawa baki 'yan gudun hijira
Amnesty International ta zargi kasashen da suka fi arziki a duniya da kin taimakawa baki 'yan gudun hijira ARIS MESSINIS / AFP
Talla

Rahotan kungiyar Amnesty International da ya yi nazari kan ‘yan gudun hijira miliyan 21 da yanzu haka ake da shi a duniya, ya ce kasashen da ke makwabtaka da inda ake samun rikice rikice ne ke daukar nauyin bakin, yayin da kasashe masu arziki suka kauda kan su.

Sakatare Janar na kungiyar Salil Shetty ya ce an barwa kasashe ‘yan kadan nauyin abinda yafi karfin su, na karbar kashi 26 na bakin.

Jami’in ya bayyana halin da ake ciki a matsayin abinda ba mai dorewa bane, ganin irin yadda miliyoyin mutane ke tserewa kasashen da ake yaki irin su Syria da Sudan ta kudu da Afghanistan da Iraqi.

Amnesty ta bayyana kasashen da suka fi daukar nauyin bakin da suka hada da Jordan mai dauke da miliyan biyu da 700,000, sai Turkiya mai miliyan biyu da rabi, Pakistan da Lebanon masu sama da miliyan daya da rabi.

Sauran kasahsen sun hada da Iran da Habasha da Kenya da Uganda da Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo da Chadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.