Isa ga babban shafi
Haiti

Guguwar 'Mathew' ta hallaka mutane 8

Guguwar Iskar da aka yiwa lakani da Matthew ta kashe mutane 7 a kasar Haiti da Jamhuriyar Dominican, yayin da ta nufi Cuba inda ta haifar da ambaliyar da ta tilastawa dubban mutane barin gidajen su.

Guguwar Mathew na gudun kilomita dari biyu da ashirin a cikin sa’a guda kacal.
Guguwar Mathew na gudun kilomita dari biyu da ashirin a cikin sa’a guda kacal. Reuters/NOAA/Handout
Talla

Wannan ya sa hukumomin Amurka suka gargadi mutanen dake bakin tekun South Carolina da su bar inda suke dan kaucewa guguwar dake tafe.

Hukumomin Haiti sun ce hanyoyin sadarwa sun katse a kudancin kasar saboda yadda guguwar dake dauke da ruwa ta lalata turakan sadarwa, da kuma rusa gadar da ta hada Port-au-Prince da tsibirin Haiti.

Guguwar Mathew na gudun kilomita dari biyu da ashirin a cikin sa’a guda kacal.
Guguwar dai itace mafi muni a tsawon shekaru kusan Goma a wannan yankin, rahotanni na cewa guguwar ta nufi kasar Cuba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.