Isa ga babban shafi
Faransa

Zanga-zangar adawa da auren jinsi a Faransa

Wani gungun jama’a da ya share tswon shekaru biyu yana adawa da auren jinsi da kuma halasta wa masu auren samun damar mallakar ‘ya’ya a karkashin dokokin Faransa,  ya gudanar da gangami a birnin Paris a jiya lahadi domin jaddada matsayinsa.

Kimanin mutane 25 suka shiga zanga-zangar adawa da auren jinsi a birnin Paris na Faransa
Kimanin mutane 25 suka shiga zanga-zangar adawa da auren jinsi a birnin Paris na Faransa REUTERS/Benoit Tessier
Talla

Masu zanga-zangar dai, sun sake dawowa kan tituna ne a daidai lokacin da aka fara yakin neman zaben shugabancin kasar.

Babban makasudin zanga zangar ita ce, nuna adawa da dokar 2013 da aka samar a karkashin tsohuwar ministar shari’ar kasar, Christiane Taubira da ta halasta auren jinsi guda.

Jami’an tsaro sun bayyana cewa, kimanin mutane dubu 24 ne suka shiga wannan zanga-zangar amma wadanda suka shirya ta sun ce, mutanen sun zarce yawan haka.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.