Isa ga babban shafi
Turai

Tarayyar Turai ta dauki mataki akan ‘Yan ci-ranin Afrika

Shugabannin Kungiyar kasashen Turai sun amince su dauki wasu matakan dakile kwararar bakin haure daga Afirka kamar yadda suka dauki matakin rage yawaitar ‘Yan gudun hijirar Syria da ke ratsowa ta Turkiya.

'Yan kasashen Afrika da dama ne ke ratsa tekun Bahrum domin tsallakawa zuwa Turai da nufin samun rayuwa mai inganci.
'Yan kasashen Afrika da dama ne ke ratsa tekun Bahrum domin tsallakawa zuwa Turai da nufin samun rayuwa mai inganci. REUTERS
Talla

Shugabannin kungiyar kasashen Turan sun bayyana daukar sabbin matakan ne taron da suka gudanar a Brussels.

Matakan sun hada da kara huldodin kasuwanci da zuba jari da kasashen Afirka da suka bada hadin kai wajen hana yan kasashen kutsawa Turai.

Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel ta ce matakin ba wai na ba kasashen kudade ba ne, sai dai kokarin ganin ‘yan kasashen Afirka sun cimma burinsu a kasashen su.

Shugabannin sun bukaci babbar jami’ar diflomasiyar kungiyar, Federico Mogherini ta fara tattaunawa da hukumomin kasashen Nijar da Najeriya da Mali da Senegal da Habasha domin aiwatar da kudirin, wanda ya kunshi amfani da jami’ansu wajen tantance ‘yan kasashensu a Turai domin mayar da su gida.

Ana sa ran gabatar da sakamakon gwajin da wadannan kasashe a taron shugabanin da za a yi a watan Disamba mai zuwa.

‘Yan kasashen Afrika da dama ne ke ratsa tekun Bahrum domin tsallakawa zuwa Turai da nufin samun rayuwa mai inganci.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.