Isa ga babban shafi
Switzerland

Bankin Switzerland na cigiyar iyalan wadanda suka ba shi ajiyar miliyoyin kudadde

Bankin kasar Switzerland ya aike da cigiyar iyalai ko dangin wasu mutane akalla 300 da suka jibge miliyoyin kudadensu na tsawon wani lokaci amma kuma ko kasa ko sama an gaza sanin inda suka shiga.

Ana  cigiyar iyalan wadanda suka jibge miliyoyin kudadde da suka kai dalar Amurka miliyan 8
Ana cigiyar iyalan wadanda suka jibge miliyoyin kudadde da suka kai dalar Amurka miliyan 8 Reuters
Talla

Mutanen da suka makare kudadensu a wannan Banki dai, sun kwashe akalla shekaru 60 ba su je ba, kuma babu wani aike game da kudaden da aka kididdige sun doshi dalar Amurka miliyan 8.

Wata sanarwa da Kungiyar Bankunan kasar ta fitar, ta ce wannan ba ya ga jerin masu asusu dubu biyu da dari shida da aka fitar da sunayen su da ake cigiya tun karshen shekarar da ta gabata.

Bayanan na nuna masu asusun sun hada da kamfanoni da kuma mutane da suka ajiye dukiyar ta su ba tare da sun waiwayi bankin ba.

Tuni dai hukumomin Bankin suka yada sunayen mutanen da kamfanonin ta yanar gizo ko dangi da ‘yan-uwan masu kudadden za su gani su tuntubi bankin don sanin yadda za a yi.

A cewar Hukumomin Bankin nan da shekara daya muddin akaji shiru, to shakka babu dukiyar ta zama ta Gwamnatin kasar Switzerland.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.