Isa ga babban shafi
Cuba

Ana ci gaba da zaman jimamin mutuwar Fidel Castro

Al’ummar kasar Cuba na ci gaba da jimamin mutuwar Fidel Castro tsohon shugaban kasar  kuma jagoran juyin juya hali wanda ya kafa gwamnatin kwaminisanci da ya rasu a daren juma'a ya na da shekaru casa'in.

Tsohon shugaban kasar Cuba Fidel Castro da ya rasu a daren juma'ar da ta gabata ya na da shekaru 90.
Tsohon shugaban kasar Cuba Fidel Castro da ya rasu a daren juma'ar da ta gabata ya na da shekaru 90. REUTERS/Charles Platiau/Files
Talla

Shugaban kasar Raul Castro ne ya sanar da mutuwar tsohon shugaban a gidan talabijin na kasar.

Gwamnatin kasar Cuba ta kuma ayyana zaman makokin kwanaki 9 don jimamin mutuwar tsohon shugaban da ya mulki kasar na tsawon shekaru 47 kafin ya janye daga fagen siyasa a shekara ta 2006 saboda rashin koshin lafiya.

Shugabannin kasashen duniya na ci gaba da aikewa da sakonnin ta'aziyyarsu zuwa ga gwamnati da al'ummar kasar ta Cuba dangane da mutuwar tsohon shugaban juyin juya hali wanda ya kafa gwamnatin kwaminisanci.

Shugaba Barack Obama na Amurka da shugaban Rasha Vlidimir Putin na daga cikin shugabanin duniya da suka bayyana alhininsu game da mutuwar tsohon shugaban na Cuba.

Nan gaba ne za'a kona gawar sa a wani karamin biki a Havana kafin a binne tokar a birnin Santiago dake kudu maso gabashin kasar a ranar 4 ga watan Disamba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.