Isa ga babban shafi
Myanmar

MDD ta ce an aikata laifukan yaki a Myanmar

Hukumar Kare Hakkin Bil Adama ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce lallai akwai alamun aikata laifukan yaki a kasar Myanmar ganin yadda ake azabtar da ‘yan kabilar Rohingya Musulumi.

'Yan kabilar Rohingya da ke gudun hijira yayin dakon shiga sansanin Kutupalang da ke kasar Bangladesh
'Yan kabilar Rohingya da ke gudun hijira yayin dakon shiga sansanin Kutupalang da ke kasar Bangladesh
Talla

Wannan na zuwa ne a dai dai lokacin da tsohon Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Kofi Annan ya isa kasar dan shirin ziyartar Jihar ta Rakhine mai fama da tashin hankali.

Ikirarin hukumar kare hakkin Bil Adama ta Majalisar Dinkin Duniya na zuwa ne bayan wani rahoto da kungiyar Human Rights Watch ta fitar wanda ke tabbatar da tserewar mutane sama da 30,000 daga gidajen su da kuma yadda jami’an tsaron suka kona gidaje tare da harbe mutane sama da 30.

Hakan ya biyo bayan tura sojoji Jihar Rakhine inda ake kallon dubban Musulmin Yankin a matsayin wadanda ba ‘yan kasa ba, inda sojojin su ka dinga afka musu su na azabtar da su, da kuma yi wa matan su fyade.

Gwamnatin kasar ta hana ‘yan jaridun kasashen duniya shiga yankin dan ganewa idan su halin da ake ciki, yayin da kuma tayi watsi da rahotannin da ake bayar wa.

Akalla ‘Yan kabilar Rohingya 120,000 Majalisar Dinkin Duniya ta ce an raba da gidajen su tun lokacin da aka fara kai musu hari a shekarar 2012.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.