Isa ga babban shafi
Faransa

Shugaba Hollande ya ce ba zai tsaya takara ba a 2017

Shugaban Faransa François Hollande ya bayyana aniyarsa ta fasa neman wani wa’adi a zaben shugabancin kasar da za a gudanar a badi.Matakin da aka jima ana jiran shugaban ya bayyana, ganin irin yadda  farin jinisa ke ci gaba da tabarbarewa a a kasar.  

shugaba François Hollande  na Faransa
shugaba François Hollande na Faransa Television via REUTERS
Talla

A cikin wani jawabi da ya gabatar wa al’ummar kasar kai tsaye daga fadarsa ta Elysée shugaba Hollande, ya yi bayani kan nasarorin da ya samu tun lokacin da aka zabeshi kan karagar shugabancin kasar Faransa a cikin watan mayun shekara ta 2012

Sakamakon da ya hada da yarjejeniyar duniya ta birnin Paris kan Dumamar yanayi, ci gaban makarantu da kuma, dokar auren jinsi daya

Sai dai shugaba Hollande ya bayyana takaicinsa guda kan rashin samun nasarar tabbatar da dokar kawo karshen mallakar takardar zama dan kasa ga wadanda ake zargi da ayukan ta’addanci a kasar.

A lokacin da yake tsokaci kan zaben fitar da dan takarar jam’iyaradawa ta Republican, Hollande ya ce, yana mutunta ci gaban da François Fillon ya samu a zaben fitar da dan takarar, sai dai a cewarsa manufar da Fillon din ya sa a gaba, zata iya haifar da babban kalubale ga tsarin zamantakewar al’ummar tare a kasar.

Manazarta dai sun bayyana dalilan da suka hana shugaba Hollande, sake tsayawa takarar neman shugabancin kasar ta Fransa, da mummunan bakin jinin da ya yi a gaban al’ummar kasar

Wanda aka ce, ba a taba yin shugaba mai bakin jini irinsa a tarihin kasar ta Faransa ba, sakamakon fito na fito da manufofin gwamnatinsa da al’ummar kasar suka sha yi ta fannonin da suka shafi tattalin arziki, ilimi zamantakewa da kuma tsaro

A ranar 17 ga wanan watan na Desember ne, jam’iyar Socialiste ta Shugaba Hollande zata bayyana sunaye masu neman ta tsaida su takarar neman kujerar shugabancin kasar a zaben na shekara ta 2017 da suka cika ka’idodin da ake bukata.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.