Brazil
An dakatar da shugaban Majalisar Dattawa kan zargin rashawa
A yau ne Kotu a Brazil ta dakatar da shugaban Majalisar Dattawan kasar Renan Calheiros, wanda na hannun daman shugaba Michel Temer ne, saboda zargin da ake masa na cin hanci da rashawa.
Wallafawa ranar:
Talla
Alkalin kotun Marco Aurelio ya bukaci aiwatar da umurnin cikin gaggawa dan bada damar gurfanar da shugaban Majalisar a gaban kotu.
Sai dai dokokin kasar sun shata cewar dole sai an samu goyan bayan mafi rinjaye na alkalan kasar.
'Yan Majalisun Brazil da manyan jami’an gwamnati na fuskantar zarge-zarge da dama na cin hanci da rashawa a kamfanin man kasar Petrobraz.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu