Isa ga babban shafi
Faransa

Christine Lagarde za ta gurfana a gaban kotu

A yau Litinin ake sa ran gurfanar da shugabar Hukumar bada lamuni ta Duniya Christine Lagarde a gaban kotu saboda zargin biyan wani attajiri kudin da suka saba ka’ida a lokacin da ta ke rike da mukamin Ministan kudin Faransa.

Christine Lagarde ta musanta zargin bai wa attajiri Bernard Tapie kudi.
Christine Lagarde ta musanta zargin bai wa attajiri Bernard Tapie kudi. REUTERS/Yuri Gripas
Talla

Ita dai Christine Lagarde ta dade ta na musanta zargin da ake mata na biyan attajirin Bernard Tapie, tsohon shugaban kamfanin Adidas da kuma kungiyar kwallon kafar Olympic Marseille makudan kudade inda ta ke cewa ta dauki matakin ne dan kare mutuncin kasa.

Wannan shari’a da ake danganta ta da siyasa ana kallon ta a matsayin wani yunkuri na batawa Lagarde suna, amma hakan bai hana ta samun cikaken goyan baya daga Hukumar Bada Lamuni ta duniya da ta ke shugabanci wadda ta ba ta wa’adi na biyu a watan Fabarairu.

Ana saran Christine Lagarde ta gurfana a gaban Kotun Jamhuriya da ke yi wa ministocin da suka saba doka shari’a.

Idan an tabbatar da laifi akan ta, ana iya daure ta shekara guda a gidan yari da tarar euro 15,000.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.