Isa ga babban shafi
Jamus

Jamus na zaman dari-dari duk da kashe Anis Amri

Shugabar gwamantin Jamus Angela Merkel ta bayyana cewa har yanzu akwai yiyuwar barazanar faruwar ayyukan ta’addanci a cikin kasar, duk da kashe Anis Amri da ake zargi da kai harin Berlin.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel EUTERS/Hannibal
Talla

Jamus dai ta bayyana kashe Amri a matsayin wani abin farin ciki, tare da kara kwantar da hankulan jama’a bayan share tsawon kwanaki uku ba tare da an san inda yake ba.

Ministan cikin gidan kasar Italiya Marco Minniti ya bayyana a lokacin wani taron manema labarai cewa, an Anis Amri mai shekaru 24 a duniya ne lokacin da ya zaro bindiga da nufin harbe ‘yansanda da ke sintiri da misalin karfe uku na Asuba.

Lamarin dai ya faru ne a kusa da wata tashar jirgin kasa da ke birnin Milan, inda ya jinjinawa ‘yan sandan biyu da suka yi wannan kokarin duk da cewa daya daga cikin ‘yan sandan ya samu rauni sakamakon harbin sa da maharin ya yi a kafada.

Kungiyar IS dai ta ce Anis Amri dan asalin kasar Tunisia, ya kai harin ne bisa umurninta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.