Isa ga babban shafi
Tarayyar Turai

Kasashen turai sun yi bikin Kirsimeti cikin matakan tsaro

Yayinda ake gudanar da bukukuwan ranar Kirsimeti a yau Lahadi, jami’an tsaro a nahiyar turai sun kasance cikin daukar tsauraran matakan tsaro, musamman a kasashen Italiya, Faransa da kuma Jamus.

REUTERS/Mussa Qawasma
Talla

A birnin Rome na kasar Italiya inda fadar Vartican ta ke, jami’an tsaro sun haramtawa, manyan motoci shiga tsakiyar birnin, zalika jam’ian sun kuma kafa shingaye bincike kan titunan da ke isa zuwa wuraren da jama’a ke taruwa.

Gwamnatin Faransa kuma jami’an tsaro da suka kunshi sojoji da ‘yan sanda 91,000 ta dauki matakin bazawa zuwa sassan kasar, hadi da daukar matakan tsaro na musamman don kare ilahirin Mujami’un da ke kasar.

Yayinda ita kuma a Jamus, matakin kara kariya suka dauka a filayen jiragen sama da tashoshin jiragen kasa, hadi da tsaurara matakan tantance wadanda ke shigowa kasar ta iyakokin kasa, duk domin kare yiwuwar barazanar kai hare-hare yayin bikin ranar Kirsmeti.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.