Isa ga babban shafi
Faransa

Ana bincike bayan kashe maharin Berlin a Milan

Hukumomin Faransa na gudanar da bincike don gano yadda Anis Amri ya ratsa ta kasar zuwa Italiya, in da aka harbe shi har lahira bayan ya kashe mutane 12 da ke cin kasuwar Kirismati a birnin Berlin na Jamus.

Jami'in 'yan sandan Italiya ya harbe Anis Amri a Milan bayan ya baro Faransa da Jamus ba tare da an kama shi ba
Jami'in 'yan sandan Italiya ya harbe Anis Amri a Milan bayan ya baro Faransa da Jamus ba tare da an kama shi ba REUTERS/Stringer
Talla

A ranar Jumma’ar da ta gabata ne, wani dan sanda Italiya ya bindige Amri mai shekaru 24, yayin da ake ci gaba da diga ayar tambaya kan yadda maharin ya fice daga Jamus zuwa Faransa kafin daga bisani ya isa Italiya.

Bayan bindige Amri, jami’an ‘yan sanda sun binciki jakarsa, in da suka gano tikitin da ya siya don shiga jirgin kasa da ga birnin Chambery da ke gabashin Faransa zuwa Milan na Italiya.

Wannan al’amarin dai ya haifar da cece-kuce game da ingancin matakan tsaro a kan iyakokin Faransa da nahiyar Turai baki daya.

To ko shin ta yaya ne maharin ya shiga Faransa daga Jamus, sannan kuma ya tsallaka Italiya ba tare da an gano shi ba duk da shafe kwanaki hudu ana neman sa ruwa a jallo a nahiyar Turai ? Tambayar kenan da hukumomi Faransa ke ci gaba da neman amsarta kamar yadda Ministan cikin gidan kasar, Bruno Le Roux ya sanar.

A bangare guda, masu ra’ayin rikau sun samu damar caccakar tsarin bude kan iyakokin kasashen na Turai saboda wannan al’amari da ya faru.

Dama dai tsarin na Schenghen ya gamu da suka saboda kwararar ‘yan gudun hijira,in da masu tsattsauran ra’ayin siyasa ke cewa, tsarin ya bude kofa ga 'yan ta’adda don samun shiga Turia kai tsaye.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.