rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Amurka Donald Trump Rasha Vladimir Putin Diflomasiya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Trump ya mayar da martani kan masu sukar Rasha

media
Zababben Shugaban kasar Amurka Donald Trump REUTERS/Carlo Allegri/File Photo

Shugaban Amurka mai jiran Gado Donald Trump ya mayar da martani kan masu sukar Rasha, tare da bayyana wadanda suka nuna adawar kulla kyakyawan dangantaka da kasar a matsayin ''Wawaye''.


Mista Trump ya bayyana haka ne a wani sakon twitter da ya aike kwana guda bayan rahotanni hukumomin leken Asirin Amurka ya bayyana cewa Shugaban Rasha Vladimir Putin ya nemi taimaka masa domin nasara a zaben kasar da ya gabata.

A cewar Trump dangantaka da Rasha abu ne mai kyau, kuma ''Mara wayo'' ne kawai zai  soki batun.

Mista Trump ya ce rawar da Rasha ta taka a zaben Amurka ba ta yi tasiri a kan sakamakonsa ba.