rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Portugal

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Tsohon shugaban Kasar Portugal Mario Soares ya rasu

media
Mario Soares, a lokacin da ya ke jan ragamar jam'iyyar socialist na Portugal a shekarar 1975 EPU / AFP

Daga gobe litinni Portugal ke fara zaman makokin kwananki Uku na rasuwar tsohon shugaban kasar Mario Soares mai shekaru 92 a wani asibiti da ke Lisbon.


Soares wanda ya yi fafutukar kafa jam’iyyar Socialist, ya kwashe shekaru yana fafatawa a fagen siyasar Portugal tare da jan ragamar shigar da kasar cikin kungiyar tarayyar Turai.

Marigayi Soares ya mulki Portugal tsakanin 1986 zuwa 1996, bayan rike mukamin ministan kasashen waje kafin ya zaman dan majlisar dokokin a Turai.

Tsohon Shugaban ya mutu ne a jiya Assabar a asibiti bayan fama da rashin lafiya.