Isa ga babban shafi
Faransa

Shugaba Hollande na Faransa ya isa Colombia

Shugaban Faransa Francois Hollande da ke ziyara a yankin Latin Amurka, ya isa Colombia a yau Litinin, in da zai gana da takwaransa Juan Manuel Santos a fadar gwamnatin kasar.

Shugaban Faransa, Francois Hollande da takwaransa na Colombia Juan Manuel Santos
Shugaban Faransa, Francois Hollande da takwaransa na Colombia Juan Manuel Santos Reuters
Talla

Kazalika shugaba Hollande zai ziyarci yankunan da za a gudanar da bikin kwance damarar ‘yan tawayen FARC don ci gaba da sabuwar rayuwa kamar sauran fararen hula a kasar.

A gobe Talata ne Hollande zai kuma ziayarci daya daga cikin yankunan da mayakan na sunkuru suka gina sansanoninsu na wucin gadi.

Za a dauki tsawon watanni shida ana amfani da shiyoyi 19 da kuma wasu yankuna 7 don karbar makamai daga hannun ‘yan tawayen na FARC.

Majalisar Dinkin Duniya ce za ta sanya ido kan wannan shirin na tattara makaman, kafin daga bisani ta tabbatar wa duniya yadda gwamnatin Colombia da ‘yan tawayen suka cika alkawuran tsagaita bude wuta kamar yadda suka yi alkawari.

Shugaban ‘yan tawayen na FARC, Timoleon Jimenez ya amince da ziyarar Hollande a matsayin wata alama da ke nuna goyon bayan kasashen duniya kan tabbatar da zaman lafiya a Colombia.

A ranar 24 ga watan Nuwamba ne shugaba Santos da Jimenez suka sanya hannu kan yarjejeniyar da suka yi alkawarin za ta kawo karshen rikicin shekaru fiye da 50 da ya lakume rayuka sama da dubu 220 a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.